China ta nuna cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soja kan Najeriya saboda zargin cin zarafin Kiristoci.
A wani taron manema labarai da aka yi a Beijing, mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen China, Mao Ning, ta yi gargadin cewa "babu wata kasa da ta kamata ta yi amfani da addini ko kare hakkin dan adam a matsayin uzuri don tsoma baki a harkokin cikin gida na wata kasa ko kuma ta yi barazanar sanya mata takunkumi da karfi."
Ta ce China ta tsaya tsayin daka tare da Najeriya "yayin da take jagorantar mutanenta a kan hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasarta."
Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya raba sanarwar China, yana mai jaddada cewa Najeriya ta ci gaba da jajircewa wajen kare 'yancin addini da kuma hakuri ga dukkan addinai.
Shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da ikirarin Trump, yana mai cewa:
"Siffanta Najeriya a matsayin wacce ba ta da juriya ga addini ba ya nuna gaskiyar kasarmu."
💬 Me za ku ce?
Shin wannan sabon babi ne a dangantakar Najeriya da China ko kuma gargaɗi ga ƙasashen yamma?

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku