Daga: Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
Yadda ake Sallar Shafa'i da Witri, sallah mai girma (Sallar da take kai mutum kusa da Allah cikin gaggawa), tare da bayani mai muhimmanci game da hukuncin sallar da tsarin ta, da kuma matsayin ta.
~ Sallar Shafa'i da Witri salloli ne da manzon Allah (S.A.W) ya bayyana cewa gara kayi su, gara a baka damar yin Shafa'i da Witri akan a baka duniya da duk abinda yake cikin ta, shiyasa manzon Allah kullum yana yin Shafa'i da Witri koda yana halin tafiya yana yin su.
Karanta Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 425.
Yaya ake yin sallar Shafa'i da Witri??.
~ Sallar Shafa'i raka'o'i ne guda biyu kamar yadda Malamai da dama suke fahimtar haka, Nana Aisha tace manzon Allah ya kasance yana karanta suratul Fatiha da suratul A'alah (Sabbi hisma) a raka'ar farko, sannan Nana Aisha tace a raka'a ta biyu kuma ya kasance yana karanta suratul Fatiha da kuma suratul Kafiruwn (Qul ya ayyu Hal Kafiruwn), idan ya kammala raka'o'i biyun sai yayi Tahiya yayi sallama, wannan Shafa'i kenan.
~ Sai kuma Witri Malamai da dama sun tafi akan cewa raka'a daya ce Tak, tare da cewa wasu Malamai suna da sabanin haka, amma jumhuwr (majority) sun ce raka'a daya ce, yaya ake yin sallar Witri?
~ Nana Aisha (a hadisin Jabir Bin Abdallah, hadisin Imamut Tirmiziy) tace "Manzon Allah ya kasance yana karanta suratul Fatiha da kuma suratul Ikhlas (Qul huwallahu ahad) sai ya 'karasa yayi sallama.
Imamun Nasa'i ya ruwaito, a Hadisi na 1,729.
~ Sannan Imamut Tirmiziy ya ruwaito Hadisi Sahiyhi cewa wani lokacin manzon Allah yana karanta Qul huwa, Falaqi da Nasi a sallar witri, dan haka ya halatta a Witri ka karanta Qul huwal lahu kadai, idan kaso kuma zaka iya karanta duka, Qul huwal lahu, Falaqi da Nasi.
Yanda ake jeranta su:
Yanda ake yin sallar Shafa'i da Witri a jerance akwai hanyoyi guda biyu kamar haka:
1. Ya halatta kayi su a jere duka ukun, amma baza ka zauna kayi Tahiya a raka'a ta biyu ba, saboda idan kayi haka tayi kama da magriba kenan, idan ka kammala raka'a ta biyu sai ka mike kawai ba tare da Tahiya ba, idan ka kammala sai kayi sallama kawai.
Karanta Sunanun Nasa'i, Hadisin na 234, a mujalladi na uku.
2. Hanya ta biyu, ya halatta kayi su daban daban, raka'o'i biyun Shafa'i daban idan ka kammala su sai kayi Tahiya kayi sallama, sai ka sake tashi kayi kabbarar harama ka kawo witrin ka, raka'a daya Fatiha da Qul huwallahu ahad, sai ka sallame.
Karanta Sunanu Ibnu Hibban, hadisi na 2,435 zaka ga Hadisin.
Daga nan sai ka daga hannu kayi ta addu'a ka fadi duk abinda kake so tabbas Allah zai amsa maka.
~ Malamai sun yi ittifaqi cewa lokacin ta ita sallar Shafa'i da Witri yana farawa ne daga bayan sallar Isha har zuwa fitowar al-fijir, sai dai idan ta kubuce maka baka yi ta ba zaka iya yin ta washegari lokacin sallar walaha, kamar yadda Hadisin Nana Aisha ta bayyana haka.
~ Sai dai anfi so ayi ta a 'karshen dare idan hakan zai yiwu, saboda manzon Allah yana cewa "Ku rinka sanya Witri ta kasance itace sallar ku ta 'karshe a dare".
Manzon Allah yace "Duk wanda yake da kyakkyawan zaton bacci bazai fi karfin sa ba, to ya bari sai a 'karshen dare yayi witrin sa, wanda kuma yake ganin bacci zai yi galaba akan sa to yayi sallar witrin sa a farkon dare".
Karanta Sahihu Muslim, Hadisi na 755, zaka ga Hadisin.
~ Sannan ya halatta kayi shafa'i raka'o'i goma, sai kayi raka'o'i goman a jere babu sallama, sai kazo raka'a ta goma sai kayi Tahiya amma ba zaka yi sallama ba, sai ka mike ka kawo raka'a 'daya witri kenan, sai ka sake zama kayi sallama, kaga shafa'in ka raka'o'i 10, witrin ka raka'a 'daya.
~ Idan kuma kayi sallar shafa'i da witrin ka a farkon dare, sai kuma ka farka cikin dare kana so ka sake yin sallolin Nafila domin neman lada, sai kayi sallolin ka amma ba zaka sake yin witri ba, saboda manzon Allah yace "Ba'a yin witri biyu a dare 'daya".
Abin nufi, idan ka tashi daga bacci cikin dare, sai ka kawo nafilfilin da kake so, amma ba zaka sake yin wata sallar Witrin ba, saboda manzon Allah yace ba'a yin Witri biyu a dare daya.
~ Sallah ce mai girman gaske wacce mutane da dama suka gafala da ita basa yi, kada ka kasance daga cikin wanda basa yin sallar Shafa'i da Witri a dare, saboda Abu Hurairah yana cewa "Masoyina manzon Allah yayi mun wasiyya cewa kada na rinka yin bacci a dare ba tare da nayi wadannan sallolin ba".
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku