SANARWA: Motar Kano Line Tayi Hatsari Akan Hanayar Ta Daga Gombe Zuwa Kano

KDK Hausa


SANARWA: Motar Kano Line Tayi Hatsari Akan Hanayar Ta Daga Gombe Zuwa Kano

A sanar da jama'a cewa an sami hatsarin mota da ya shafi daya daga cikin motocin hukumar sufuri ta jihar Kano (Kano Line) da ta tashi daga tashar Dankwambo Mega Park a Gombe da safiyar yau zuwa Kano.

Shugaban hukumar sufuri ta jihar Gombe, Malam Sani Sabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bukaci 'yan uwa da su ziyarci ofishin Kano Line domin duba sunayen fasinjojin da ke cikin motar (manifest).

Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan cikakken adadin mutanen da abin ya shafa, tare da fatan samun rahama ga wadanda suka rasu.

"Allah ya jikan wadanda suka rugamu gidan gaskiya, ya kuma ba wadanda suka jikkata saukin jiki," in ji Malam Sani Sabo.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku