Gwamnatin Jihar Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta fara shirin gudanar da auren jama’a ga ma’aurata 2,000 a karkashin shirin tallafin auratayya na jihar.
Wannan mataki dai na daga cikin kokarin gwamnatin jihar wajen tallafawa matasa da marasa karfi domin rage yawan mata da maza marasa aure a cikin al’umma, tare da bunkasa zaman lafiya da kyakkyawar tarbiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar Hisbah za ta fara tantance wadanda za su amfana da shirin nan ba da jimawa ba, domin tabbatar da cewa an yi wa dukkan wadanda suka cancanta rijista kafin a gudanar da bikin.
An kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kayan aure da sauran bukatu na ma’auratan da za su shiga cikin wannan shiri.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku