KA RIBACI ABUBUWA BIYAR KAFIN ZUWAN ABUBUWA BIYAR.
-
Manzon Allah ï·º, ya ce, ku ribaci abubuwa guda biyar kafin zuwan wasu abubuwa biyar É—in.
-
▪️Ƙuruciyarka kafin tsufanka.
▪️Lafiyarka kafin rashin lafiyarka.
▪️Wadatarka kafin zuwan talaucinka.
▪️Lokacinka kafin zuwan rashinsa.
▪️Rayuwarka kafin mutuwarka.
Sahih at-Targeeb (3355)
-
"Duk wani mai tunanin da yasan me yake yi, kuma yasan abin da ya kawo shi duniya, to haƙiƙa yakan kiyaye waɗannan abubuwan kuma yakan ci ribarsu kafin ya rasasu, saɓanin wannan kuma, shi ne yake banzatar dasu yake tozartasu, baya taɓa sanin muhimmancinsu har sai lokacin da ya rabu dasu"

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku