Zaɓen ƙananan hukumomi: Magoya bayan PDP na zanga-zanga a Rivers

KDK Hausa


Zaɓen ƙananan hukumomi: Magoya bayan PDP na zanga-zanga a Rivers 

Rikicin siyasar jihar Rivers ya ɗau sabon salo a yayin da magoya baya da mambobin jam'iyyar PDP a jihar suka fantsama tituna suna zanga zangar adawa da zaben kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 5 ga watan Oktkba na 2024.

Masu zanga zangar tun da farko sun haɗu a saakatariyar jam'iyyar dake birnin Fatakwal da safiyar Alhamis kafin su hau kan tituna don yin zanga zangar.

Leadership ta rawaito cewa bayanan dake dauke da kwalayen masu zanga zangar ya nuna magoya bayan ministan Abuja, Nyesome Wike ne.

Idan za a iya tunawa dai, Gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya ayyana hutu a yau Alhamis da gobe Juma'a a jihar don bai wa al'umma damar zuwa yankunan su don yin zaben na ranar Asabar.


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku