"Matawalle Ba Shi Ne Mai Tallafa Mana Ba," Jawabin Bello Turji Ya Wanke Tsohon Gwamna —Kungiya

KDK Hausa


"Matawalle Ba Shi Ne Mai Tallafa Mana Ba," Jawabin Tùŕjì Ya Wanke Tsohon Gwamna —Kungiya

Kungiyar Al’ummar Arewa Concerned Citizens of Nigeria ta bayyana cewa Allah ya wanke Ministan Jiha na Tsaro, Bello Matawalle, bayan da mashahurin shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, ya ce babu wanda ke tallafa musu, ciki har da Matawalle.

An yi imanin cewa Turji ya tsere daga Zamfara bayan sojoji sun ƙara kaimi wajen kai hari kan ‘yan ta’adda a jihar, kuma ya bayar da sharuddan zaman lafiya a Zamfara.

Ya ce zaman lafiya zai dawo a jihar idan jami’an tsaro da ‘yan banga sun daina kai hari da kashe Fulani a Zamfara da wasu wurare.

Ya yi wadannan kalaman ne a cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a ranar Litinin.

“A lokacin mulkin Yerima ne gwamnati ta sayar da filayen kiwo kuma ta halatta kashe Fulani. Lokacin da Mahmoud Shinkafi ya hau mulki, ya yi ƙoƙarin magance matsalar amma bai yi nasara ba. Abdulaziz Yari ya ba wa ‘yan banga ƙarfi, amma har yanzu muna fama,” in ji Turji.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin da rana, Kwamared Mansur Abubakar, ko’odinetan ƙasa na kungiyar, ya ce, "Dole ne mu yarda da matsalolin tsaro da rashin adalci da suka dade suna damun mu.

"Daga mulkin Yerima, wanda ya sayar da filayen kiwo kuma ya halatta tashin hankali kan al'ummar Fulani, zuwa mulkin da suka zo daga baya da suka kasa samun mafita mai dorewa, a fili yake muna bukatar shugaba mai hangen nesa da azama."

A cewarsa, Gwamna Matawalle ya tabbatar da kansa a matsayin irin wannan shugaba. Ya bullo da matsalar rashin tsaro da nufin gaske, yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da neman zaman lafiya ta hanyar shawarwari da matakai na karshe.

Yayin da shugabannin baya suka bai wa ‘yan banga damar aiki ba tare da magance tushen matsalolin ba, Matawalle yana aiki don samar da mafita mai dorewa da zai amfani kowa, yana haɓaka zaman lafiya da fahimtar juna.

"Kokarin gwamnatinsa na rufe gibin da kuma magance matsalolin tarihi sun nuna sadaukarwarsa wajen gina makoma mai cike da tsaro da mutunta kowa.

"Gwamna Matawalle yana zama kamar fitilar bege, yana jagorantar mu zuwa Zamfara mai zaman lafiya da haɗin kai. Mu goyi bayansa, mu tallafi burinsa, kuma mu ci gaba da tafiya a ƙarƙashin jagorancinsa mai ƙarfi da tausayi," in ji Mansur.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku