Farashin Shinkafa ya sakko a kasuwar duniya

KDK Hausa


Farashin Shinkafa ya sakko a kasuwar duniya

Farashin shinkafa ya sakko da kaso 20, mafi karanta cikin shekaru 16 acewar bayanan da kungiyar masu fitar da shinkafa ta duniya suka fitar .

Nairametrics ta rawaito cewa saukar farashin ya biyo bayan matakin da kasar India ta dauka na baya bayan nan na sassauta dokar hana fitar da shinkafa daga kasar.

Kasancewar ta kasar da aka fi fitar da shinkafa zuwa Asia da Afrika, matakin na India ya taimaka wajen sakko da farashin shinkafar zuwa farashin ta na 2008.

Yankin Afrika dai shi ne yafi kowanne yanki shigo da farar shinkafa daga kasashen India da Thailand.

Kasashe irin su Senegal da suka dogara da shigo da shinkafa daga India zasu fi amfana da matakin.

Matakin kuma, ana sarai zai sassauta farashin kayan abinci a yankin.


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku