Ku guji auren daya daga cikin irin matan nan

KDK Hausa


KA GUJI AUREN D'AYA DAGA CIKIN SU.

1- Kada Ka Yarda Ka Auri Macen Da Iyayenta Suka Tilasta Mata Aurenka, Don Kawai Su Suna Sonka,

2- Kada Ka Auri Macen Da Kace Kana Sonta, Sannan Ka Tambayeta Shin Itama Tana Sonka? Sai Ta Amsa Maka Da: Mutum Ai Bazaiki Mutum Ba, 

3- Kada Ka Auri Zabin Wani, Ba Zabinka Ba,

4- Kada Ka Auri Macen Da Take Zagin Maza, Domin Bisa Ga Dukkan Alamu Ta Samu Babban Rauni Daga Wurin Namiji, Wannan Raunin Warinsa Zai Dinga Cutar Dakai Lokaci Bayan Lokaci,

5- Ina Kashedinka Da Babbar Murya, Ka Guji Auren Macen Da Bata Tsoron Iyayenta, Domin Ba Zaka Gane Illar Ace Mace Bata Tsoron Iyayenta Ba Sai Bayan Sabani Ya Shiga Tsakanin Ku Bayan Kunyi Aure, A Sannan Zaka Rasa Inda Zaka Kai Kararta Inda Za'a Tankwarata Tare Da Bata Umarnin Yi Maka 'Da'a

Ubangiji Allah Ya Zaba Mana Mata Nagari Wadanda Musulunci, Iyayenmu, Yan Uwanmu Tare Da Abokananmu Zasuyi Alfahari Da Ita Bijahi Sayyaduna Rasulullahi Sallallahu Aaihi Wasallam


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku