Naziru Sarkin Waka A Cigaba Da Fadawa Masu Mining Gaskiya Koda Ba Sa So
....kuma Naziru ya fi karfin a kira shi da dan maula domin ya baiwa naira milyan 500 baya
Ra'ayin Sadeeyerh Bilerl
Duk da cewa Sarkin Waka ya shiga gonar masu mining wajen fadar albarkacin bakinsa, har suka maida masa martani cewa dan maula ne ko maroki ne ko dan hassada ne.
Shin ko zaku iya sani cewa Naziru bai dauki waka sana'a ba, nishadi ya dauki waka ce a gunsa, kuma sannan ya fi karfin a ce masa dan maula domin yaba naira miliyan dari biyar baya.
Na tabbata Naziru zai iya kyautar miliyan biyu ba tare da ya ji ciwon kai ba, kudin da wani har ya gama mining ba zai samu ba.
Sannan Naziru bai dogara da waka ba, duk abunda ka gani ya samu a waka ba roka ya yi ba ganin dama aka yi aka ba shi.
Sannan Naziru yana da sana'a wacce ba lalle ya fadawa duniya ba, domin manomi ne, kuma yana harkar kasa ya siya ya sayar.
Shawara ta ga 'yan mining ita ce idan kun dauki ra'ayi ko shawarar Naziru shi kenan, idan kun ki ku cigaba da mining dinku baki alaikum, kawai shi dai ra'ayinsa ya fada.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku