Gwamnatin Jihar Kano Zata dauki Lauyoyi guda Saba’in 70 aiki domin inganta harkokin Shari’a A Jihar Kano.

KDK Hausa


Gwamnatin Jihar Kano Zata dauki Lauyoyi guda Saba’in 70 aiki domin inganta harkokin Shari’a A Jihar Kano.

Tin bayan da Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yaba da umarnin daukan Lauyoyi guda 70 aiki, domin inganta harkokin Shari’a A Jihar Kano, tini Kwamitin tantance daukan Ma’aikatan Karkashin Jagorancin Famanan Sakatare kuma Babban Mai gabatar da kara na Gwamnati (Solicitor General) na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano Barr. Mustapha Nuradden Muhammad.

Da yake Jawabi Barr. Ya bayyana cewa ba’a taba daukan Ma’aikata guda 70 a lokaci guda ba, wanda Ya ce tin a shekarar 2017 lokacin tsohuwar Gwamnatin da ta gaba ta dauki Ma’aikata guda 20 ba’a kara dauka ba Sai yanzu karkashin Umarnin Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif, Barr. Mustapha yace Gwamnan ya ja hankalisu kan Kaura cewa Alfarma, a tabbatar an dauki cancanta domin inganta harkokin Shari’a a fadin Jihar Kano.

A karshe Barista yace kuma Gwamna yace za’a cigaba da daukan Ma’aikatan har sai an tabbar da wadatar Lauyoyin Gwamnati a Ma’aikatar Shari’a Ta Jihar Kano.

Amir Abdullahi Kima Senior Special Reporter Justice to the executive Governor of Kano state H.E Abba Kabir Yusuf 
11/06/2024


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku