KANNYWOOD TA SHIGA SAHUN MANYAN MASANA’ANTUN SHIRYA FINA-FINAI NA DUNIYA A shekarar 2024.
Daga Abdussamad Ishaq
Ko shakka masana’antar kannywood ta zama shakundum, musamman yanda wasu ke kokarin ganin sun kaita ga gaci.
Fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau ta kafa tarihin da tun farkon kafa masana’antar yau kimanin kusan shekaru 25, a iya cewa babu wanda ya kafashi kuma ta shiga tarihin da baza’a taba mantawa dashi ba, muddin za’a ambaci sunan masana’antar.
Film dinta (movie) ya kai ga har anfara haskashi a manhajar nan ta Netflix wanda ayanzu ma sun sauya sunan cover profile dinsu zuwa film din WAR, wanda itama jaruma sadau tana ciki, kuma hakan nada nasaba ne da fina finan da take ciki suka bayyana a manhajar ta Netflix, wanda tsahon kafuwar wannan manhaja film din hausa bai taba zuwa can ba.
Kuma Alhamdulillah wannan shi ake kira from AREWA TO THE WORLD, don hakan zai bada dama a kalli harshen hausa a fadin duniya kamar yanda ake kallon fina finan INDIA, har ake fassara su zuwa harshen hausa.
Tabbas sadau ta cancanci jinjina ta musamman daga makallata dama abokan kasuwancinta na masana’antar kannywood.
FIM DIN MATI A ZAZZAU YA SAMU KULAWA TA MUSAMMAN DA KAYAN AIKI, HADI DA JARUMAI WADANDA SUKA BADA GUDUMMAWA FIYE DA ZATO.
Sai dai muna fatan a gyara yan kalubalen da suke masana’antar kamar yanda na bayyana a tattaunawata da sashin hausa na Daily Trust
Jinjina ta musamman ga Umar Gombe Adam A Zango Saddiq Sani Saddiq da fitacciyar mawakiyar nan Dija.
Kuma anyi amfani da wakokin mawaki SarkinWaka wanda suma sun bada gudummawa wajen fito da al’adar kasar hausa tsantsarta.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku