WANNAN MAGANAR YA DAINA TSORATA KI, MAZAJEN AURE SUNYI KARANCI.

KDK Hausa



WANNAN MAGANAR YA DAINA TSORATA KI, MAZAJEN AURE SUNYI KARANCI. 

Ke ga shawarwari na gare ki. 

👉🏻 Ki kasancewa baiwar ALLAH, mai tsoron UBANGIJIN ki, mai dogaro gare sa matukar dogaro. 

👉🏻 Ki kasance baiwar ALLAH mai riko da Sunnah Manzon ALLAH (saw), ki nisanci shirka, bidi'a, ki nisanci saɓon ALLAH daga kan, rashin sallah ko wasa da sallah, ko wasa da karatun Alkur'ani, ko biyawa kai buƙata, ko zina ko luwaɗi, ko mummunar hali, ko zamo wa ke ga ki sai mu'amula da maza ko yawo zuwa gidan biki ko zuwa gidan mutane ke ga ki kullum fita, ki nisanci wa'ennan dabi'u.

👉🏻 Ki kasance baiwar ALLAH mai kokari ibada, neman ilmi, kyawawan halaye, saboda ALLAH, ki kasance mai tsafta mai karancin magana, mace mai aji, neman ilmin addini da na boko kada ki wasa, ki kula da kwalliya yadda bai saɓawa Shari'a ba, ki kasance mai matukar biyayya ga iyayen ki mai zaman lafiya, ki nisanci kawayen BANZA, na hane ki da yawaita kawaye, kada ki yarda ki kasance kawa ga wacce take wasa da addini.

👉🏻 Ki koyi sana'a duk kankantar sa, na hane ki da zamo wa mai son abun duniya, mai kwaɗayi ki tsaya a matsayin ki matukar tsayawa, ki dogara ga ALLAH, ki sanya suturar da ALLAH ya hore miki, ki riki wayar da ALLAH ya hore miki, kada ki kasance ke wai dole sai kin siya abun yayi, wallahi ko da wayar ki ba ta da internet ki hakura ki rike.

👉🏻 Ki kyautata zahirin ki da kuma boyen ki, idan ALLAH ya baki Wanda ke sonki da aure, matuƙar na gari ne mai sana'a aure shi, dayawan mutane suna arziki ne bayan aure, babu wata daraja mafi kyawu mafi kusanta wa ga ALJANNAH fiye da aure. 

👉🏻 Kisani macen kirki ba ta taɓa rasa mijin aure, ki riki azzkhar ki nemi tsarin ALLAH daga kowanne Sharri, ki nemi dacewar sa daga kowanne alkhairi, ki dogara ga ALLAH kina Kai mishi kukan ki, kina yawaita istigfa'ri da hailala da salatin manzo da nafilfili musamman na dare ko da raka'a biyu ce, Na rantse da ALLAH UBANGIJI zai datar dake da mijin aure na gari, ki dogara ga ALLAH.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku