WAJE BIYAR (5) DA DAN ADAM KE AMFANA DA AYATUL KURSIYYU

KDK Hausa


WAJE BIYAR (5) DA DAN ADAM KE AMFANA DA
AYATUL KURSIYYU

1. Karanta kafa daya (1) kafin fita daga gida, Allah Zai aiko Mala'iku dubu saba'in (70,000) su tsare ka/ki har sai ka/ki koma gida.

2. Karanta kafa daya (1) kafin shiga gida, talauci bazai shigan maka/ki gida ba

3. Karanta kafa daya (1) bayan alwalla, darajar ka/ki zata daga sau saba'in (70) a wajen Allah

4. Karanta kafa daya (1) lokacin kwanciya, Allah Zai aiko Mala'ka daya (1) ya tsare ka/ki har lokacin daka tashi

5. Karanta kafa daya (1) bayan kowace Sallar farillah, mutuwa kawai zata hana ka/ki shiga Aljannah.

Ma'ana da zaka/ki mutu a wannan lokacin Aljannah zaka/ki kai tsaye insha Allahu Allah Ya bamu dacewa, amin summa amin.

YAWAN AMBATON ALLAH YAYIN KWANCIYAR BACCI. 

Yana kara lafiyar bacci cikin nitsuwa,
Bacci cikin nitsiwa yana kara kaifin hankali,
Kaifin hankali kuma yana sanya kyayyawan tunani, 
Kyayyawan tunani kuma yakan sanya mutum yaji tsoron Allah, 
Tsoron Allah kuma yakan sa mutum ya kyautata ayyukan sa,
Kyawawan ayyuka kuma suna sa mutum ya dace da Rahamar Allah. 
Saida Rahamar Allah ake shiga Aljannatul firdaus. 
Allah ya sa mu dace. 

Duk wanda yayi share Allah ka biya mishi bukatun shi na alkhairi.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku