KU SAURARA 👂👂👂
Sayyiduna Usman ɗan Affan (R.A) ya kasance duk lokacin da aka binne gawa a gabansa, sai yayi ta rusa kuka kamar ransa zai fita!
.
Mutane suka tambaye shi; "Ya kai sarkin muminai, mai yasa kake yin kuka akan ƙabari, alhali ana mutuwa a gabanka amma baka yin irin wannan kukan?"
.
Sai yace: "Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Ƙabari shine masaukin farko daga masaukan lahira. Idan ya kasance alkhairi, to abinda ke bayansa yafi shi alkhairi, idan kuma ya zamanto sharri, to abinda zai biyo bayansa yafi shi sharri".
.
A cikin wani Hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) yana cewa; "Ƙabari yana ce ma ɗan Adam yayin da za a sanya shi cikinsa: "kaiconka ya kai ɗan Adam, waye ya ruɗe ka daga tunani na!
.
Shin baka san cewa ni ne gidan fitina ba? Kuma gidan duhu, kuma gidan kaɗaitaka, kuma gidan tsutsotsi?" "Wane ne ya ruɗe ka har ka kasance kana wucewa ta kusa da ni lokuta masu yawa?".
.
Ya Salaam! Wannan ranar tana nan tana jiran kowan ne daga cikinmu. Kuma babu mai taimakonka sai alkhairin da ka aikata.
.
Ya Allah kasa mu cika da imani. Ya Allah kasa mutuwa ta zama hutu a gare mu. Ya Allah kasa ƙabarinmu ya zamanto dausayi ne na Aljannah. Ya Allah ka yalwata mana ƙabarinmu ka sauƙaƙa hisabinmu.
.
Ka kiyaye mu daga tashin hankali a ranar Alƙiyamah ka sanya mu a cikin ceton fiyayyen bayinka, Annabin mu Masoyinmu Shugabanmu Muhammadu (sallallahu alaihi wasallam).
________________________
Allah sa mu dace. Amin

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku