KARATUN MACE!
Yau da safiya a labarai nake jin wani bawan Allah ya saki matarsa ƴar shekaru goma sha huɗu (14), saboda namiji ya ƙarbi haihuwarta a jahar Katsina. Kuma ƴan uwanta sun ce tasha wahala ne a gida, shiyasa aka kaita asibiti domin taimakon gaggawa.
Shi koh tausayinta baiyi ba, ga ta yarinya ƙarama, ga haihuwa, ga rauni, bai damu da lafiyarta ba.
Irin wa'innan mutanen ne suke maida Al'umma koma baya, basu barin matansu koh Æ´aÆ´ansu suyi karatun boko, amma suna so wasu suyi sai su duba lafiyar Æ´aÆ´ansu mata da matansu.
Idan har kana so mace ta dinga kula da lafiyar matarka, toh kaima dole ka bada gudummawa wajen kai Æ´aÆ´anka mata suyi karatun boko.
Shi karatun bokon mace ba dole sai tayi aiki ba, amma ka duba makomar Æ´aÆ´anka. Ilimin mace ya zama dole.
0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku