Matukar ana son soyayyah tana ginuwa da kauna har a kai ga matakin...

KDK Hausa


Soyayyah na mutum biyu ne...

Babu fa Yadda za'a ana soyayyah amma ace mutum daya ne yake yi,dole ne daga macen har Namijin kowa ya bada nasa gudumawar.

Kulawa da junan ku,idan daya shi kadai yake yi,daya ba yayi,to za'a iya samun matsala dole ne dayan ya gaji.

Amma mutum biyu sune masu soyayya gaskiya,kowa yana bukatar kulawan Dan uwan sa.

Mace idan ita daya ne take damuwa dakai,ya zama kai baka damuwa da ita koda ace kana son ta,to wannan rashin kulawan da zaka na bata,zata fara tunanin baka son ta koda ace kana son ta da gasken,wata ma take zata kyale ka domin tana ganin ba son ta kake yi ba.

Haka bangaren Namiji shima, idan shi kadai ne mai wahala da ke yana kulawa bakya damuwa dashi, shima zai fara tunanin bakya son sa yakan duba wata kawai.

Kunga duk ku biyu din nan kun kashewa kan ku soyayyar ku, saboda rashin kulawa da junan ku.

Matukar ana son soyayyah tana ginuwa da kauna har a kai ga matakin mallakar junan ku, to dole ake kiyaye a kuma fahimci juna.

©️ Nusaiba Tasiu Nusaiba Tasiu Abdulrahim

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku