MATASA GA MAFITA GUDA 5
Tabbas nayi rayuwa irin naku kuma yabani wahala sosai, amma dai cikin taimakon Allah ga yadda nayi na samu mafita, shiyasa nace kuma bari na sanar daku saboda wasunku zasu gwada, Allah yasa muyi daidai 🤲
Sau da dama a samartana nayi fama da sha'awa sosai, gashi kuma bana yadda naci abinci laga-laga, sannan kuma banaso nayi abinda dana sani zai biyo baya, amma ga matakan dana É—auka guda 5 saboda neman mafita, kuma tabbas nadace tun kafin na gama!
1) Abinda na farayi shine ƙarawa kaina imani, na cirewa kaina wasi-wasi akan lamarin Allah, wallahi a wannan lokacin tsaban yadda na kiyaye sallah 5 a wuni, akwai wasu mutane da idan suka ganni to Azahar yayi, haka suka ɗaukeni a matsayin lokutan sallolinsu 5, saboda wallahi kafin a ƙira sallah ina ƙofan masallaci, haka kuma da dare bana yarda har gari ya waye ban tashi nayi sallah dare ba, wallahi akwai lokacin da zan iya cewa Allah yana turowane a tasheni, saboda har mamaki nakeji, yadda nake farkawa da dare, sannan kuma ina gane lokacin sallah darene da kukan zakaru, saboda nasan suna kukane da dare idan sukaga mala'ikun Rahma! Abinda nake so na faɗa muku shine ku kiyaye salloli 5 tare da sallah dare yadda yakamata!
2) Kada cikin nemanka kayita amfanar da kanka babu taimakon iyaye a ciki, ko sadaka, sannan kuma ka taimaki wanda yazo da buƙata na tsanani, koda zuciyarka ya tunama wani abu, to kayi masa domin Allah kuma domin Allah ya taimaki rayuwarka!
3) Kayi ƙoƙari wajen samar da sulhu tsakanin mutane da kuma kanka, duk wanda kukayi ba daidai ba dashi ka bashi haƙuri, sannan ka nuna masa kaine da laifi, kuma kaci gaba da mu'amalantar sa yadda ya dace, tare da yimasa kyakkyawar zato.
4) Ka sabarwa bakin ka yawaita Istigafari, Astagfirullahal azim Astagfirullah wa'atubu ilaihi, kokuma Astagfirullah, Astagfirullah, kokuma Astagfirullahal azim laa ilaha illah huwal hayyul ƙayyum wa'atubu ilaihi.
5) Ka yawaita zama da tsarki, kuma ka guji taɓa najasa, ka ajjiye dukkan abinda kakeyi na laifi, ka

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku