Kin kashe shi kina Nadama, Gashi kema Bakya raye Duda kina Numfashi.
•Tunda Ya ganki Ya furta yana sonki.
Ya tura a tambayo masa Auran ki.
Ya tara Abokai suna murna Da Aurar ki.
Yau a silar ki tasa baya Numfashi.
•Ko Ina yaje cikin Abokai Labarin ki.
Yayi Gwagwarmaya domin Aurar ki.
Sana'a kala-kala domin mallakar ki.
Yau sheÉ—an ya taya ki kin kashe shi.
•Yau baya raye mene ne Ribar ki.
Ya bar Duniya ke nadama na kanki.
Me kike tunani ga Dangi In sun kalle ki.
Rabbi ya yafe masa kurakuran shi.
•Yanzu rayuwa ki tana Æ™unci.
Kona babu mai baki Abinci.
Hatta zaman fira saidai kiyi naci.
Ƙuncin rayuwa yanzu kika fara.
•Duniya zatai Miki zafi.
Ko ina kika je Akwai su da zafi.
Ba tausasa harshe sai mai zafi.
Ƙarshe kuma babu Auran ki.
"Sunana HABIBU MAKOLE. Nayi wannan saƙon domin ku fahimci daga lokacin da kika kashe mijin ki to kema Bakya raye Duda kina numfashi domin kullum mutuwar zaki na roƙawa kanki Irin halin da zaki shiga ko fita waje bazaki iya ba zaki ƙare rayuwar ki kamar baiwa mara gata ƙashe kije kiyi Nadama a Lahira"
Allah ka shiryar damu.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku