*WASIYYOYI* *GUDA 5 DAGA* *MANZON
ALLAH*
*(S.A.W).*
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Waye zai karbi
wadannan Kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi Amfani da su, ko ya
Sanar
da wanda zai yi Amfani da su"
Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni Zan karba ya
Ma'aikin
Allah.
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike Hannu na
yace min:-
1. Ka guji Aikata Sabo, Zaka Zamo wanda yafi
kowa Bauta a cikin Mutane.
2. Ka yarda da Abinda Allah Ya baka, Zaka fi
Kowa
Arziki Cikin Mutane.
3. Ka kyautata wa Makobcin ka, Zaka Zamo
(cikakken) Mumini.
4. Ka So Wa Mutane Abinda Kake So Wa
Kanka, Zaka Kasance (cikakken) Musulmi.
5. Kada ka Yawaita Dariya, Domin Yawan
Dariya na
Kashe Zuciya.
"Manzon Allah (S.A.W) Yace Ka Rike su Ko ka
Sanar da Wanda Zaiyi Amfani
Dasu".
Idan ka Tura Wa 'Yan Uwa Musulmai Baka
San Wa Zaiyi
Amfani Dasu Ba, Kaga Ka Samu Ladan
Mutane Masu Tarin
Yawa.
Ubangiji Allah ya bamu ikon aikatawa
Mohammed Tasiu Abubakar

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku