Tsarin kudi ya lalace a karkashin Emefiele – Shugaba Tinubu

KDK Hausa


Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fasa yin shiru kan dakatarwar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yayi.

 Ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni, yayin wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa da makwaftan kasashen Turai, a gefen taron sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudade ta duniya da aka yi a babban birnin kasar Faransa, Paris.

 Shugaban ya ce tsarin kudi na kasa karkashin dakatarwar Emefiele ya lalace. Ya kara da cewa ‘yan Najeriya da dama a kasashen waje ba sa iya aika kudi ga ‘yan uwansu saboda yawan kudin canjin da ake samu, inda ya ce yanzu ya zama tarihi.

 An dakatar da Emefiele daga aiki ne a ranar 9 ga watan Yuni, kuma tun a lokacin yana hannun DSS.
 “Tsarin kudi ya lalace. Mutane kadan ne ke yin jakunkuna na kudinmu sannan kai da kanka ka daina aika kudi gida ga iyayenmu talakawa. Window da yawa… amma wannan ya tafi yanzu, ya tafi. Mutumin yana hannun hukuma, ana yin wani abu a kan hakan, za su daidaita kansu.” Yace


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku