SHIGAR TSIRAICI DA AMARE KEYI, LAIFIN IYAYE NE KO LAIFIN ANGWAYEN SU.?
Daga Auwal Wadata Sansan
.
Abun yakan ban mamaki matuka, sai kaga ranar auren mutum gashi bahaushe kuma musulmi kuma wadda zai aura itama musulma amma sai kuga shigar su tasha bamban da tarbiya da ko yarwar Addinin Musulunci
Daga gefe guda sai kaga Ango yayi Shiga ta kamala yayi shiga ta mutun taka, amma ita kuma amaryar sai kaganta kamar wata aljana, gata yar musulmi amma tayi Shiga wadda ko "ya"yan arna basayinta a ranar auren su.
A haka fa gasuda iyaye kuma suna gani, amma sunata sakin baki, kamar sakarai ya bude fanfo baisan dabarar rufewa ba, sun saki amanar da Allah yabasu.
Shin iyaye kun manta amanar da Allah yabaku, shin meye amfanin ka faranta ran yarka amma kuma kasabawa mahalicinka, kabar yarka tayi Shiga kamar tsohuwar karuwa, tafita tsirara da nufin murnar ranar aurenta, shin aure hauka ne meye amfanin haka.?
Shawarata gareka ango yakamata kayi kishin tsiraicin matar ka, kudaina yarda da mummunar shigar da sukeyi suna batawa addinin musulunci suna, sannan kaima angon wannan mummunar shigar tana zubar maka da mutunci.!
0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku