Saudiyya da Amurka sun ce za su iya dage tattaunawar da aka shirya....

KDK Hausa


A jiya Asabar ne, Saudiyya da Amurka suka bayyana a wata sanarwar hadin gwiwa cewa bangarorin biyu da ke rikici da juna a Sudan sun amince da wata sabuwar tsagaita wuta ta sa'o'i 72.
Tsagaita wutar ta fara aiki ne daga karfe 6:00 na safiyar yau Lahadi agogon cikin gida wanda yayi daidai da karfe (0400 GMT).
Sanarwar ta ce, bangarorin biyu masu rikici da juna sun amince su kaurace wa yin amfani da karfin soja da kuma kai hare-hare a lokacin tsagaita bude wuta.
Sun kuma amince da ba da damar zirga-zirga ba tare da tsangwama ba da kuma kai kayan agaji a duk fadin kasar.
Saudiyya da Amurka sun ce za su iya dage tattaunawar da aka shirya yi a Jeddah idan har bangarorin biyu da ke rikici da juna suka kasa kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
A ranar 15 ga Afrilu ne mummunar tashin hankali ya barke tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun sai kai na RSF a babban birnin kasar Khartum da wasu yankuna.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar ‘yan Sudan fararen hula 958 tare da jikkata wasu 4,746, a cewar sanarwar da kungiyar likitocin Sudan ta fitar a ranar Laraba. 

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku