Mun rushe shataletalen gidan gwamnati me saboda akwai zanen ƙaton kuros a jikinsa -- Baffa Bichi

KDK Hausa


Mun rushe shataletalen gidan gwamnati me saboda akwai zanen ƙaton kuros a jikinsa -- Baffa Bichi

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Baffa Bichi, ya bayyana karin dalilan da suka sa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wani katafaren shataletale na kofar gidan gwamnati.

Sai dai da ya ke magana a gidan rediyon Freedom Kano wanda DAILY NIGERIAN ta saurara, Bichi ta ce shataletalen na ɗauke da wani karon kuros a jikin zanen sa, wanda a cewarsa ya sabawa akidar Musulunci.

Bichi ya kara da cewa tsarin ya na kuma kawo cikas ga yadda direbobi ke shiga duk hanyoyin da suka hada da shi.

“shataletalen na kawo cikas ga masu ababen hawa, na biyu kuma, idan ka yi amfani da na’urar daukar hoto mara matuki, za ka ga cewa yana ɗauke da babban zane na kuros a samansa.

“Kuma sama da kashi 9.99 ko 100 na ‘yan Kano Musulmai ne. Don haka ba za mu yarda a yi gini da kuros a jiki ba. Ya sabawa kimar Musulunci.

“Malamanmu sun gaya mana cewa, duk lokacin da Annabinmu Muhammadu ya ga wani abu, komai kankantarsa, da alamar kuros, zai tabbatar da an raba shi," in ji shi.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku