Malamai sun ce daga cikin dalilin da yasa Maza suka zama Maza shine saboda karfin hali da suke dashi da dauriyar ciyarwa da kashe Kudaden su wa iyalan su, suka ce wanda baya iya kashe kudin sa ga iyalan sa dai dai gwargwadon halin sa bai cika cikakken namiji ba, Maza basa tsoro, shakka ko jin nauyin kashe kudin su don amfanin iyalan su, har a cikin Suratun Nisa'i Allah yace:
الرجال قوامون على النساء بما فضل الله بعضهم على بعض وبما أنفقوا من أموالهم
Suka ce a wajen zamantakewa Kudi shine yake sa ka a gane ka zama Namijin gaske ne ko kuma kaima photo copy din Maza ne?
~ Mai karamin shekaru idan yana iya kashe kudin sa wa iyalan sa don jin dadin su, wannan babba ne kuma namiji ne. Wanda kuma bai iya kashe Kudin sa wa iyalan sa don kyautata musu komai yawan shekarun sa sai dai ace masa "Happy Childrens Day" don ba babba ne wannan, 'karami ne.
~ A cikin Ayar nan ta Suratun Nisa'i Allah ya bayyana cewa dama automatically Allah ya daukaka darajan Maza, a dalili na biyu dake nuna Maza sun fi Mata shine wajen iya kashe Kudin su don amfanin iyalan su, wanda bai iya kashe kudin kuwa toh idan yafi mace ma toh sai dai karfin jiki kawai ya fita, photo copy din Maza kenan ba asalin namiji ba.
~ Rashin kashe kudin ga iyalai yana daga cikin kalubalen da yake kawo broken homes a cikin society, musamman ga wanda yake da hali, yake da Kudin da zai kashen idan baya kashewar.
~ Sai kaga 'ya'ya sun tashi a lalace, tarbiyyar su ta tawaya saboda rashin sakin Kudin Mahaifin su akan su, lafiyar gangar jikin su sai ta samu nakasu, kallo da fahimtar da ake yi musu a cikin gari da Unguwa sai ta gagara kaiwa matsayin da ya dace a kalle su, matar sa ko Matan sa sai su koma matsayin da bai dace da ace iyalan wane ba kenan.
~ Amma fa kashe kudi ga iyalai ba shine ayi wa mace matar gidan duk abinda take so ba, kula da iyalai ba yana nufin ayi miki duk abinda kika ce ayi ba. Domin wata takan dauka idan ba ayi mata abinda ta tsara a zuciyar ta ba toh Mijin ta baya kula dasu.
~ Menene wajibin rayuwa, menene farillan rayuwar gidan, me za ayi ya zama anyi shukan da gobe za'a girbe cikin farin ciki shine kula da iyalan. Mazaje sukan samu kansu a wasu yanayin da ba lallai su iya aiwatar da komai ba, musamman a yanzu da rayuwar tayi tsada, hanyoyin samu suka matse sosai.
~ Musamman a yau da duk namijin da ka ganshi da iyalai toh bayan su akwai wadanda kuma suke jira ya taimaka musu, kenan ba iyalan ne kadai akan sa ba, dole sai iyaye mata sun dinga kallon wannan.
~ Allah ya datar damu, ya buda ma wadanda suka cikin kunci da iyalan su, wadanda zuciyar su tayi nauyi wajen biyan bukatun iyalan su Allah ya bude zuciyar don iyalan su samu mafita na alkhairi daga gare su.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku