Magoya bayan madugun 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko sun yi arangama da jami'an tsaro, bayan da aka yanke wa Sonko hukuncin dauri a Dakar, 2 ga Yuni, 2023.
A ranar Juma'a ne aka tura dakarun soji zuwa sassan Dakar babban birnin kasar Senegal a daidai lokacin da birnin ke ci gaba da samun karin tarzoma bayan daurin kurkuku kan madugun 'yan adawa Ousmane Sonko ya haifar da daya daga cikin kwanaki mafi muni na tashe-tashen hankula a kasar a baya-bayan nan.
An kashe mutane tara a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da magoya bayan Sonko a ranar Alhamis bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa. ‘Yan adawar dai sun ce hukuncin da ka iya hana Sonko tsayawa takara a shekara mai zuwa na da nasaba da siyasa.
Jami’an tsaro sun yi ta sintiri a titunan da babu kowa a ranar Juma’a amma cike da kone-konen motoci da duwatsu da fashe-fashen gilashin da ke cike da lalata gidaje da wuraren kasuwanci. An yi jigilar manyan gungun dalibai daga harabar jami'ar.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku