Labari Kan Dogariyar Matar Mataimakin Shugaban Kasa Ba Gaskiya Ba Ne
Daga Mati Shehu
Labarin da wasu jaridun online suka wallafa akan dogariyar uwargidan mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima ba gaskia bane.
Mun yi magana da mawallafin labarin Adam Hassan KNC inda shi ma yafadi cewa labari ne wanda baida makama ballantana tushe!
Mu gujewa fadawa irin wannan hadarin ko daukar labaran karya domin ita matar mataimakin shugaban kasa mutuniyar kirki ce, ita kanta dogariyar tana da nata matsalar wanda inda tayi aiki baya wani bazaiso yayi aiki da ita ba ko kadan.
Mace mai kamala irin Nana Shettima matar tsohon Gwamna ce, kuma tsohon Sanata. Dole akwai bincike da bayanai wanda za su iya iske ta akan wanda zai aiki da ita. Tana da ‘yanci, amsa ko yadda, ko kin yadda da wanda zatai aikidashi ba irinsu waccar dogorin ba.
Gaskiyar zance shine Nana Kashim Shettima tana da dogari da masu kama mata aiki tun kafin Kashim Shettima ya zama mataimakin shugaban kasar Najeriya, domin matar tsohon Gwamna ce, kuma tsohon Sanata. Tana da masu mata aiki, bata bukatar dogarinda Gwamnnati ta sake kawo mata.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku