KAFIN HATSARIN JIRGIN RUWAN KWARA ,KANA DA LABARIN JIRGIN JOOLA A SENEGAL ?
Shine hatsarin jirgi mafi muni da aka taba samu, amma ko kadan Manyan jaridun Duniya basu bashi muhimmanci ba.
Shekaru ashirin da suka wuce jirgin ruwa mai suna joola ya nitse a ruwan Gambia a hanyarsa ta zuwa Dakar daga south Senegal.
Mutane akalla 2000 sun mutu,adadin da ya ninka na jirgin Titanic amma mutane kalilan suka san labarin a wajen Senegal.
A ranar 26 na Satumbar 2002 jirgin joola ya koma Senegal bayan shafe kusan shekara ana gyaransa.
An kera shi a kasar Germany aka Kai shi Senegal a 1990.
Joola ya kasance yana zirga-zirga daga southern Senegal, Zinguinchor, har Dakar.
Rashin kyan hanyoyi da saukin sha'ani ya sa mutane ke son hawan Joola da ke ratsawa ta Gambia.
Ranar da abin ya faru a cika jirgin fiye da kima a Zinguinchor.
Cikin mutune 2000 mace daya ce Mariam Diouf ta tsira da wasu mutane akalla ashirin.
Yara 444 suka rasa rayukansu a wannan jirgi.
Hatsarin ya girgiza ahali masu yawa cikinsu akwai fitaccen Dan kwallo Aliou Cisse Wanda ya rasa mutum 11 harda yayarsa.
Abin takaici har yanzu ba'a ciro wannan jirgi don fitar da wadanda suka mutu ba sai 'yan kadan da ruwa ya fitar daga ciki.
Ya Kamata a rage yawan mutane da ake diba fiye da kima a jiragen ruwa.
Allah Ya gafarta musu

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku