Idan Namiji ya tashi son yaudaran ki ko rabuwa dake.....

KDK Hausa


Idan Namiji ya tashi son yaudaran ki ko rabuwa dake.....

1. Zaki ga yafara canja miki bakamar yadda kuke dashi ba,Sam zai fara fito miki da wasu halayya wanda baki san dashi ba.

2. Zai fara kirkiran fad'a a tsakanin ku,ko abu baki masa komai ba zai fara cewa kin masa yana dai son abinda zai haÉ—a ku fad'a dashi.

3. Zai daina baki kulwa da yake miki, idan yana kiranki ko kuma chat zai daina,idan kin masa magana zai nuna miki shi baida lokacin ki bayan kuma yasan kina son sa.

4.wani zai bijiro miki da abinda yasan bazaki iya ba,misali ya ce,ki masa sex chat ko ki tura masa nude pic naki, Kuma yasan kina da tarbiyya bazaki iya ba,idan kika nuna masa bazakiyi ba zai ce a rabu.

5.wani kuma bama zaki sani ba sai dai kika invitation card na auren sa,idan kin masa magana sai ya nuna miki haÉ—a su akayi alhalin kuma karya ce kawai salon yaudara ce.

Yar uwata to sai me? Idan ya rabu dake ya yaudare ki,lallai zaki ji ciwon hakan a zuciyar ki wanda idan bakiyi tawakkili ba sai ki saka damuwa a zuciyar ki, Wanda zai iya haifar miki da matsala,amma Kuma idan kika jure, kikayi hakuri da sannu Allah zai kawo miki mafi alkhairi a cikin rayuwar ki,wanda zakiyi farin ciki.
Hakkin yaudarar daya miki da sannu sai kiga Allah ya miki sakayya.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku