Hira Mai Ratsa Zuciya daga Majalisar Annabi Muhammad (SAW)
.
Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta
Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?
Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_
1: zama a gaban ka,
2: kallon ka,
3: ciyar da dukiya ta gare ka.
Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki
Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?
Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_
1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne,
2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,
3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.
_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_
_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_
1: ciyar da abinci ga mabukaci,
2: yada sallama,
3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.
_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_
_Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_
1: Azumi a lokacin rani,
2: Karrama bako,
3: yakar abokan gaba da takobbi.
_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_
_Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
1: yunwa,
2: jinya,
3: mutuwa.
_Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_
Sai Aba zarri yace:
*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi,
*ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na
_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
1: isar da sako,
2: bayar da amana,
3: son nakasassu.
_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku