HALIN DA TALAKA MAGIDANCI MAI 'YAYA BIYU KE CIKI A NAJERIYA

KDK Hausa


HALIN DA TALAKA MAGIDANCI MAI 'YAYA BIYU KE CIKI A NAJERIYA
   

Bayan nazari da bibiyar yan uwa da abokan arzuka, bayanin dake tafe shi ne bayanin halin da Magidanci mai 'yaya biyu ke ciki.

ABINCIN SAFE

Bread N600
Kosai N300
Ruwan Shayi ba Madara N200
Total: N1,100
A wata N1,100 x 30 = N33,000

Ko kuma

Ka yi wainar fulawa
Flour N400
Mai N250
Maggi N100
Kayan Miya N50
Kamu/ Kunu N200
Sugar N150
Gawayi N100
Total: N1,250
A wata N1,250 x 30 = N37,500

ABINCIN RANA

Spaghetti daya da rabi N600
Mai N150
Maggi N80
Kayan Miya N70
Gawayi N70
Total: N970
A wata N970 x 30 = N29,100

ABINCIN DARE

Idan za ka yi tuwo Kwata/rabin rabin tiya
Gari N250
Maggi N80
Kayan Miya N70
Mai N100
Kuka N80
Daddawa N50
Gawayi N100
Total: N730 x 30 = N21,900

RUWA

Ruwa N150 x 30 = N4500

A DUK WATA MAGIDANCI YANA KASHE N88,500 idan zai sha Shayi ba Madara kuma ba zai ci kifi ko Nama ba. Idan kuma wainar fulawa zai yi da safe zai Kashe N93,000 shi ma dai banda Kifi da Nama.

Kada mu manta lissafin magidanci mai 'yaya biyu ne, kuma ba mu saka wadannan abubuwan ba

1. Kudin Haya
2. Kudin wuta
3. Rashin Lafiya
4. Kudin zuwa aiki
5. Omo, Sabulu da sauran su
6. Kudin Makarantar yara na Boko
7. Kudin Makarantar yara na Islamiyya.
8. Banda kayan sakawa


Hikimar ita ce mu koma ga Allah Mu Gyara.Allah yakawomana Sauki Acikin Wannan kasa tamu


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku