Duk yadda wayar ka takai da ɓata maka rai saidai ka cilla ta Aljihu ko kasamu kan gadon ka ka wulla ta nan ma sai ka tabbatar katifar mai laushi ce.
Idan babu caji kai ta neman inda zaka cazata Ido rufe ka siya mata Rigar waya da wasu matakan kariya koda zata je faɗuwa su kare ta.
Idan ta lalace baza kai shawara da kowa ba zaka nemi kuɗi ka gyaro kayar ka har tofa mata yawu kake ka goge ta domin tayi kyau.
To Fiyeda haka Ake so ka riƙe mace wallahi Mallam wasu sun ɗauki kulawar mace sun ɗorawa waya Gwargwadon yadda ka kula da ita gwargwadon yadda zata kula da kai kowa yanda hakki Akan kowa kuma kowa Abin tambaya ne a Ranar Lahira.
Allah Yasa kada wasu su fahimce ni ba dede kuma suƙi tambaya ta.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku