Daga Karshe Hukumar DSS Ta Kama Gwamnan Babban Bankin CBN, Emefiele Bayan Kokarin Da Ya.....

KDK Hausa


A wani lamari mai ban al’ajabi da yammacin Juma’a, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), jim kadan bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa.

 Matakin da shugaba Tinubu ya dauka na dakatar da Emefiele bai bai wa mutane da yawa mamaki ba, domin kuwa gwamnan babban bankin na CBN ya sha suka a kan yadda ya ke tafiyar da harkokin kudin kasar.

 Wata sanarwa da ta sanar da dakatar da shi ta ce matakin ya zo ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a ofishinsa da kuma shirin yin gyare-gyare a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.

 Willie Bassey, Daraktan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ya ce dakatarwar Emefiele na nan take.

 Bayan dakatarwar, hukumar ta DSS ta yi gaggawar cafke Emefiele, inda ta kai shi gidan yari domin amsa tambayoyi.

 WHISTLER ya tuna cewa an tuhumi Emefiele da laifin taimakawa da kuma ta’addanci kuma hukumar DSS ta yi yunkurin kama shi bai yi nasara ba kafin shugaba Tinubu ya hau mulki.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku