Ƴan sanda sun kama mahaukacin bogi a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani matashi Abubakar Ali mazaunin unguwar Gwale tare da wasu mutane biyu a Kotu.
Ana zargin Abubakar da yin shigar Mahaukata yana sayar da miyagun ƙwayoyi a Gwale.
Sai dai bayan ɗaukar lokaci ƴan sanda na bibiyarsa a ƙarshe sun gano mahaukacin bogi ne.
A kan hakan ne aka gurfanar da shi a Kotun Shari'ar Muslunci da ke Fagge Ƴan Alluna ƙarƙashin jagoranci mai shari'a Malam Umar Lawan Abubakar.
Ƴan sandan sun kuma gurfanar da wasu mutane biyu Muhammad Sabi'u da Muhammad Abubakar bisa zarginsu da sayen ƙwayoyi a wajen Abubakar.
An karanta musu tuhumar da ake musu kuma sun amsa nan take.
Kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin wata shida-shida ko tarar Naira Dubu goma-goma.
Sannan a tsatstsala musu bulala ashirin-ashirin kowannensu.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku