Abubuwa Shida Atakaice da ke Wanzar da Farin Ciki Kuma Yake Sa Azauna Lafiya da Mace

KDK Hausa


Abubuwa Shida Atakaice da ke Wanzar da Farin Ciki Kuma Yake Sa Azauna Lafiya da Mace___




Hakika Kowace ’Ya Mace Imma ta Cikin Gida “Matar Aure” ko ta Waje “Budurwa” Suna Bukatar Wadan nan Ababen Guda Shida daga Wajen ’Da Namiji, rashinsu ke Tarwatsa Zamantakewar Aure ko Soyayya .

Dukkan Namijin da ke Son Zama Lafiya to Lallai Ya Wajaba Masa Ya Liximci Aikata Wadan nan Ababen guda Shida.

1. Mata Suna Son Kyautatawa da Kulawa.
2. Mata Suna so arika Nuna Musu ana Sonsu ana Kaunarsu Cikin Furuci da Aiki.
3. Mata basa Son Mutum Mai Tsanani ko Mugun Takurawa.
4. Mata Suna Son Irin abin da Namiji Yake So daga Gurin Mace.
a. Daddad‘ar Kamshi
b. Magana Mai dad‘i
c. Kyakkyawar Shiga
d. Tashin Kamshi, dss.
5. Mata Suna Son A Mika Musu dukkan Mukamai na Sarauta, Sannan Kar Ka Yarda ka Rusa Wannan Sarutar da ka dorawa Masarautar.
6. Mata Sun Kasance Masu Son Yabo Kalamai Masu Tausasa Zuciya a Yayin Gabatuwar Kunci.
_____________________________________________

Masoyi: “Idan Kuka Lura da Ya Mace, tana da Matukar rauni, Hakan Ke Sanya Suke Wa Maza rarraunan hidima a Wani bangaren, ku kuji hantara da Nuna Musu Basu Kai ba, ko Ai Kuke da Mukami, iko Yana gareku Su ko Suna Kasan Mulkinku.

Ya Isheka Abin Girmamaws ga ’Ya Mace, idan Ka Tuna Wata Rana fa ita ma Uwa ce ! 

Allah Ta'ala Yasa Mu dace, Duniya da Lahirarmu

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku