Abinda nakeso nace shine, Kada ka ɗauki Mataki akan wasu kalamai da....

KDK Hausa


WANI ABU SAI YA'YA MATA 
።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።
_ Mace zata iya yin Blocking Dinka, takuma goge Lambarka sannan tace kada Ka kara kiranta har Abada. Amma sai ta koma gefe tana jiran ganin sakonka. Kada ka tambayeni Dalili, domin matane kadai zasu iya yi maka Bayani.
።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።
_ Ɗan uwa inaso ka Sani ita fa Macen da take mutukar kaunarka da Gaskiya zata iya yin "Blocking" Dinka a WhatsApp, Facebook, sannan ta dinga karbar wayar kawayenta tana dubawa taga yadda kake tafiyar da Al'amuranka ko Don taji sanyi cikin ranta.
።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።
_ Zasu iya furta maka munanan kalamai da nuna cewa alaka ta Kare a tsakaninku a gabanka. Amma a gefe guda zata kwaranyar da Hawaye Mai radadi a saboda kaunarka. Zuciyar Mata na da Mutukar taushi fiye da tafukan kafar Jariri.
።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።
_ Abinda nakeso nace shine, Kada ka ɗauki Mataki akan wasu kalamai da Mace ta Furta maka a Lokacin da take cikin fushi, domin mafi yawan Lokutan da suke cikin fushi abinda suka furta ba shineh har cikin Zuciyarsu ba.
።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።
Dan Allah aringa tausayawa mata tare da lallashinsu tamkar kwai
Allah ya tabbatar da al'khairi agaremu 
ALLAH YAKARAWA ANNABI DARAJA S A W AMEEN  
 ።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።።

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku