Yau a ka ƙaddamar da matatar man fetur ta Dangote, mafi girma a Afirka. Za ta fara tace mai a watan Yuni.
Ku na ganin kafa wannan matatar man zai kawo ƙarshen wahalar man fetur a Nijeriya?
Labari mai daɗi ga yan Najeriya musamman matasa.
Shugaban kamfanin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce sabuwar matatar man da ya gina zata ɗauki ɗaruruwan dubbannin mutane aiki.
Yayin kaddamar da matatar man Fetur din yau Litinin, Ɗangote ya ce sabuwar matatar zata samar da da ayyukan yi fiye da tunanin mutane.
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci kaddamar da matatar a jihar Legas ranar Litinin 22 ga watan Mayu, 2023.
Matatar man Dangote da za ta soma aiki daga wannan Litinin, za ta rika samar da ganga dubu 650 a kowace rana don ba wa ‘yan Najeriya, kama daga Man Dizel da Kalanzir zuwa ga Fetur da Man Jirgi.
Shugabannin kasashen Afirka shida ne ake hasahen za su halarci bikin kaddamar da matatar man a jihar Legas ciki har da Shugaba Bazoum na Nijar da Nana Akufo na Ghana da Macky Sall na Sénégal da Shugaba Yadema na Togo a wannan Litinin.
Akwai kuma fitattun ‘yan siyasar Najeriya ciki har da Sanata Kwankwaso da zababben gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da sauransu.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku