Yanda wasu maza suke yaudarar mata kan.....

KDK Hausa


KAR KI BARI YA RUDE KI


1.duk wani dadin bakin sa da zai miki don ki sallama masa kan ki,kar kiyi wannan mungun kuskuren,karki fara karki yarda da wannan dadin bakin sa na yaudara,duk lokacin daya samu wannan damar ki koka da kanki.

2.kiyi tunani kiyi nazari ki gani,shi wannan saurayin dake kokarin ganin ya rabaki da mutuncin ki wannan ai ba saurayin kirki bane,kuma ba mutumin da zai aure ki bane,idan har kina kula wannan mutumin akwai matsala gaskiya.

3.ki kara kokartawa ganin duk wani saurayi wanda ba mutumin kirki bane kin rabu dashi.

4.wani daga fara furucin sa zaki iya fanimtar abinda yake so,karki yarda da wani soyayyar sex chart domin daga nan za'a iya zarcewa ayi mai gaba dayan.

5.duk abinda zai kashe miki ko zai miki duk wani wasar da zaiyi miki da dukiyar sa,in dai bawai son aure yake miki ba, karki yarda domin duk na banza ne lokacin da zai gama yayin ki a lokacin zaki dawo kina danasani.

6.kiyi kokarin ganin kin tsira da mutuncin ki Wanda iyayen ki suka baki,wani can wanda baisan muhimmancin ki ba, baisan wahalar ki ba ya cutar da ke.

7.ki tsira da mutuncin ki saboda Allah,kiji tsoron haduwar ki da Allah.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku