Wato wannan wani samfuri ne na yadda ake yin shooting a lokacin da za a fitar da wani film

KDK Hausa



-
"Wato wannan wani samfuri ne na yadda ake yin shooting a lokacin da za a fitar da wani film"
-
"Ku dubi yadda ake lalata tarbiyyar iyayen mu mata, ku dubi yadda su kuma suke zubar da mutuncinsu a idon duniya"
-
"Babu ta yadda za ayi mace tayi irin wannan abun a gaban namijin da ba muharraminta ba sannnan kuma ace bazai yi sha'awar yin lalata da ita ba idan suka keɓe, babu ta yadda za ayi ace an ƙare wannan shooting ɗin ba tare da namiji ya taɓa ta ba"
-
-
"Ke mace ce mai daraja, tunda Allah ta'ala ya yi ki musulma, to haƙiƙa ya yi ki mai daraja, ya rage naki ki tsare mutuncin kanki, kada neman kuɗi ko shuhura su sa ki zubar da ƙimarki a gurin Allah maɗaukakin sarki"
-
"Lallai ki sani; su waÉ—anda suke sanya ki ki zubar da mutuncin na ki a gabansu, baza su taÉ“a kawo Æ´a'Æ´ansu, ko Æ™annensu, ko Æ´an’uwansu mata na jini cikin wannan banzar harkar ba"
-
"Lallai ki sake sani; tabbas ke ma ƙuruciyarki kawai suke yin amfani da ita, a yanzu suna sha'awarki ne kawai, suna sha'awar shigar banzan da kike yi ne a gabansu"
-
"Tabbas ki san da cewar; shekerunki suna ɗan ƙara ja, za su watsar dake su nemo wata yarinyar mai jini a jika, a sunyi miki adalci shi ne su dinga ɗaukarki kina fito musu a film a matsayin MAMA, wato ke zamaninki ya wuce kenan"
-
"Wannan rawar da girgiza jikin da kike yi a cikin film, tamkar kina lalata ƙimah da darajar ƴa'ƴanki ne, domin su ma abin sai yayi ta'asiri a cikin rayuwarsu"
-
"Ina so ki sake sanin cewa; a lokacin da aka sanya miki camera ana ɗaukarki hoto ko bidiyo, to tamkar kina aikatawa ne a gaban kowa a zahiri, domin baki san adadin dubunnan jama'ar da za su kalleki kina tiƙar rawa ba, baki san adadin jama'ar da za su kalleki namiji yana taɓa jikinki ba, wataƙila har da malamin islamiyyarku sai ya ganki, ko limami unguwarku, ko ƴa'ƴanki, ko iyayenki. Kinga kuwa tarbiyyar ki ai batayi aiki ba a nan"
-
"Ni dai yanzu kirana ga Æ´an’uwana mata da maza masu wannan wasan kwaikwayon, suji tsoron Allah ta'ala, susan cewa haÆ™iÆ™a Allah buwayi yana kallonsu, kuma sai ya tambayesu a bisa dukkanin abin da suke aikatawa na fili da na É“oye"
-
"Mata ku kare mutuncin ku, domin haƙiƙa babu rayuwa mafi hatsari irin rayuwar mace, matuƙar baki tattali mutuncinki ba, to haƙiƙa kina kusa jin kunyar duniya da kuma ta lahira"
-
Allah ta'ala ya kare mana mutuncin mu baki É—aya, yasa Æ´an uwanmu mata su gane cewa harkar film ba harkar tarbiyya bace, Allah ya dawo dasu hanyar daidai baki É—aya, Ameen.
-

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku