Wata bugaggiyar direba ta kaɗe amarya ta mutu jim kaɗan bayan daurin aurenta

KDK Hausa


Wata direba da ke tuƙi cikin maye ta kashe wata amarya mai suna Samantha Miller, wacce take motar Golf din da amaryar da ango ta ke ciki a South Carolina, kamar yadda hukumomi su ka bayyana a jiya Litinin.

A cewar ofishin masu bincike na Charleston County, amaryar, ƴar shekaru 34 da aka daura wa aure sa’o’i kadan da su ka gabata, ta mutu a cikin motar, inda hakan ya yi sanadiyyar jikkata wasu uku a cikin motar golf din, ciki har da ango, wanda ke kwance a asibiti kuma yana cikin mawuyacin hali.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa mahaifiyar ango ta kirkiri wani asusu na GoFundMe don biyan kudin jana’izar surukarta da kuma kudin maganin ɗan ta.

Ta hada da hoton sabbin ma’auratan da suke nishaɗi cikin motar daf da faruwar haɗarin, wanda ya sa motar korar golf ta rika juyawa.

Bayanan da aka samo daga wacce ake zargin, motar ta haya ce ta Jamie Lee Komoroski ta nuna cewa tana tuƙi a matakin gudu na 65.(kilomita 105 / h), kuma a takaice kawai ta taka birki kafin ta buga motar golf da misalin karfe 10 na daren Juma’a a kan Folly Beach, in ji masu binciken.

Gilreath ta ce motar golf din na da fitulu kuma ya halatta a tuƙa ta da daddare.

Iyakar gudun kan tsibirin kusa da Charleston shine 25 mph (40km/


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku