Daga : Usman Bin Adam
Hakan yasa naga ya dace na kara tunatar damu akan haka"
GA KADAN DAGA IRIN TAMBAYOYIN"
1 Shin kana son alqur'ani ko a'a ?
2 Idan kana son annabi muhammad S'A'W kada ka wuce baka rubuta S'A'W ba"
3 Ko kuma idan kana son annabi muhammad S'A'W kada ka wuce ba kayi comment da S'A'W ba"
Gaskiya bai dace ariqa ire iren wayannan tambayoyin ba" kai yin suma jahilci ne"
Kuma akwai wasu photunan fima fimai na wulakanta alqur'ani da addinin Allah" da wani sashi na kafurai sukeyi ana samun wasu daga cikin musulmai suna tayasu ya dawa" to hakan bai dace ba" kai yin hakan ma taimakawa kafuran ne akan aikinsu na kafurci"
Sannan akwai wasu rubututtuka da ake ya dawa ana umurtan mutane da tsoritar dasu da rudar dasu da sunan wai mutum zai samu wani abu na duniya" za kaga ana turawa mutane ace kaima ka turawa mutum goma ko ashirin zaka samu karin matsayi a gurin aikinka" wani da ya tura ya samu matsayi akwana uku" wani kuma da yaki turawa sai aka koreshi a gurin aikinsa"
Biyayya akan bin ire iren wayannan mutanen yana saka imanin mutum ya yi kasa" domin kuwa mai cikekken imani ba zai musu biyayya ba" saboda yasan da cewa da mutanen duniya zasu hadu guri guda domin su amfanar da shi wani abu" ba zasu iya amfanar da shi komai ba sai abin da Allah ya kaddara a gareshi"
Kuma yasan da zasu hadu guri guda domin su cutar da shi wani abu ba" ba zasu iya cutar da shi komai ba sai abin da Allah ya kaddara a gareshi"
Dan uwana kace babu abin da zai same ka sai abin da Allah ya rubuta maka domin shine ubangijinka" kuma gare shi muminai ya kamata su dogara"
Ya Allah ka tsare mu fadawa cikin kowani irin halaka" ya Allah ka dauki rayukanmu akan imani" kasa mucika da kalman shahada Amin

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku