Wanne Irin Tasiri 'Hasken Screen' Yake Dashi ga Lafiyar Ido?
Gaskiyar abinda yake haifarwa da kuma yanda mutum zai kare kansa.
Mafi yawan mutane suna zaton yawan anfani da screen "yana rage karfin gani" wanda hakan ya sha ban-ban da abinda kwararrun likitocin ido da kuma binciken kimiyya suke fada.
Yawan anfani da na'ura me screen kamar waya ko computer ya zama jiki awannan zamanin, shi kuma screen din yana dauke ne da Blue Light, a haka zakaga kamar farin haske ne amma kuma blue ne.
Kwararrun likitocin ido suna fada cewa hasken screen (blue light) yana da tasiri ga lafiyar Ido kamar haka:
1. Computer Vision Syndrome: Yawan anfani da blue light screen yana haifar da wani abu da scientifically ake kira da 'Computer Vision Syndrome' (CVS), Shi kuma CVS dinnan yana rage yawan kiftawar idanu da mutum yake yi wanda hakan yake haifar da bushewar ido da zaka rinka ji kamar idonka ya bushe kamar babu 'giris' , baka jin dadin kiftawa da motsawarsa, wanda shima hakan zai saka masa gajiya.
A karkashin wannan CVS mun samu abubuwa guda uku da yawan anfani da Blue light screen yake haifarwa.
2. Ƙarancin 'Milatonin Hormone' a Kwakwalwa: yawan kallon Blue light Screen yana haifar da ƙarancin 'Milatonin Hormone' a kwakwalwar mutum, shi kuma Milatonin Hormone shi yake kula da tsarin baccin mutum, wanda karancinsa zaisa tsarin baccin ya canza, ya zama ba ka iya bacci a lokacin daka saba kana yi, ko kuma bayan ka kwanta baccin ba zai yi tsayi ba.
Idan ƙarancin Milatonin Hormone yayi yawa yana iya haifar da cutar damuwa, ƙibar data wuce kaida, da kuma Cardiovascular disease.
Wadannan abubuwa sune abinda likitoci suka tabbatar cewa Blue light screen yana haifarwa.
Hanyoyin da mutum zai iya kare kansa sun hada da:
1. Yin anfani da Dark Mode ko Eye Care akan screen, wanda shine zai rage karfin Blue light din.
2. Yin anfani da screen awaje mai haske sosai idan dare ne, kar ya zama Hasken Screen din ya bayyana.
3. Bayar da tazara tsakanin ido da screen, kar ya zama kusa da ido sosai.
4. Hutu a yayin anfani da Screen, kadan tsayar da abinda kake ka huta minti 10 zuwa 20 hakan zai rage tasirin Computer vision syndrome.
5. Dena anfani da screen na lokaci mai dan tsayi kafin lokacin yin bacci, don rage aukuwar karancin Milatonin Hormone a kwakwalwa.
6. Yin anfani da Blue Light Eye Glasses, suna taimakawa sosai wajen rage tasirin blue light din ga idanu.
Daga karshe dai wadannan sune abinda ilimi ya tabbatar, yawan anfani da screen ba ya rage ganin mutum, kuma baya haifar da wani abu na zahiri da za'a iya gani a ido, kuma na'urorin da muke anfani dasu waya da laptops bincike ya tabbatar ba suda 'Ionizing Radiation' da sauran electrical devices suke dashi wanda yake iya cutar da lafiyar mutum.
Bayan binciken da nayi, as a patient, personally naga kwararrun likitocin ido dayawa, daga cikin likitocin akwai wanda na tambaya kuma ya tabbatar min cewa kallon Screen ba shida alaka da lafiyar Gani na.
Allah ya tsare mu ya bamu lafiya mai anfani ba wacce zamuyi nadamarta ba.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku