Turawa suna cewa "There is a Power in naming" wato akwai karfi ko karfafawa da kake bayarwa mutum idan ka ambaci suna sa ko an kira sunan mutum a bainar Jama'a. Wato duk sadda kake adawa da wani mutum, ko baka son sa ko kake sukan manufar sa toh idan ka kama sunan sa directly kana 'kara masa karfi da isa da jin kai, kuma ka 'kara tallata shi a cikin jama'a kenan.
~ Shiyasa zaka gani ko a cikin Al-Qur'ani me girma, munafukai da suka addabi Manzon Allah a zamanin sa wadanda suka dinga cin dunduniyar Musulunci sai Allah yaki ya kira sunan su a cikin Ayoyin Al-Qur'ani da ake saukar wa Manzon Allah a wancan lokacin.
~ Sai dai kaji Allah yace و منهم wato "Daga cikin su", ko kuma وان منهم wato "tabbas daga cikin su", Allah yaki ya kama sunan su, saboda there is a power in naming, akwai power din da kake bayarwa mutum idan ka kira sunan sa.
~ Rashin kiran sunan su kai tsaye a cikin Al-Qur'ani yana bakanta musu Rai, yana 'Kona musu zuciya. Wannan wani irin Uslubi ne da a galibin lokuta ake amfani dashi domin Binne abokin adawa ba tare da ya sani ba.
~ Wani lokaci mutane da yawa basu san wane ba sai in ka ambace shi zasu sani, daga lokacin wasu zasu samu interest akan sa, me yasa? saboda ka bashi Power ta dalilin kama sunan sa.
~ Makiya Manzon Allah da suka yi ta kokarin kashe Manzon Allah sai Allah ya dinga cewa "Zaka gane su da alamar tuntuben harshe idan suna magana" sai yayi amfani da furucin (هم) wato "Su", anki a kira sunan su.
~ Rashin Hikima ne a yau kaga mutum yana kama sunan wanda yake adawa dashi ko sunan jam'iyyar sa a cikin dubban mutane ko a Shafin da kake da Followers mutane dubu kaza kuma kazo ka kama sunan su ko saka hoton su ko Videos dinsu.
~ Misali, zaka ga mutum ya fito ya soki shugaban kasa ko Gwamna an kyale shi, zai fito yayi ta bakaken maganganun sai su kyale shi, Kai sai kace wallahi idan nine sai nasa an kamo shi. Idan kasa aka kamo shi shike nan ka Kara masa daukaka. Baku Gani ba a kasar nan aka yi ta zagin wani shugaban kasa Amma yayi shiru..
~ Amma matar sa da aka taba a social media sai tasa aka kamo Wanda ya soke ta din, bayan kwana uku da kama shi mutane Miliyan nawa ne suka San shi? Mutane dubu nawa ne suka yi masa kyauta? Naira nawa ya samu?
"There is a power in naming".
~ Dan haka koda irin 'yam mata marasa kunya masu koyar da batsa ko rawar banza a social media ko a Film kuskure ne ku kama sunan su ko ku saka hoton su ko Videos dinsu, kuma basu Power ne, kuma abinda kuke so ku kashe ko ku dakile ba za ku iya dakilewa ba, saboda kuma kama sunan su, kuna saka hoton su da Videos din su da sunan gyara ko Nasiha.
~ Wannan dai wani Uslubi ne da idan aka gwada amfani dashi za'a dakile abubuwa da yawa da kuke so ku dakile a siyasa ko a Addini ko a tarbiyyar da take tangal tangal a cikin al-ummar ku.
✍️
Abdul-Hadee Isah Ibraheem.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku