Tallata Tsaraicin Ƴaƴa Mata Na Ɗaya Daga Cikin Hanyar Fara Zinace-Zinace Ga Ƴaƴa Maza
Daga Ibrahim Y. Ibrahim
Yau she ne wasu ƴaƴa matan za susan cewa? Cikar darajar su shi ne lulluɓe wannan tsaraicin da su mayar da shi abin ado a yanzu. Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da su yaba surar jikin ki? Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suyi sha’awarki da burin sai sun keta miki Haddi ko ta wani hali? Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suke shauƙin tunanin surar jikin ki? Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da suke yabon gaɓa-gaɓa na sha shin jikin ki? Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ kin san adadin mutanen da su fara sha’awar fara Zina? Da lilin bayyanar da tsaracin ki‚ in san adadin mutanen da su faɗa irin wannan rayuwar na tallata tsaraici ga duniya a social media? Kin zama abin koyin su wurin yaɗa baɗala.
Kuma duk domin a samu followers da zama celebrity Duniya sanki. To Albishirin ki‚ duk wanda ya zama kece sanadin saɓon mahalicin sa‚ kina da kason zunubin baɗalan da ya aikata‚ domin sanadin ki ya saɓama Allah ta’ala. Duk tarin fillowers ɗin nan‚ da mutanen da su sanki a duniya wurin tallata tsaraicin ki‚ ze yi wuya su miki addu'a koda sau ɗaya ne in kin mutu. Saboda kin yi suna a duniya ta hanyar saɓon Allah da ta’ata da lalata tarbiyyar al’umma. Abin tambaya anan shi ne‚ mi ye ribar tallata tsaraici ga duniya? Na’am ana samun kuɗi‚ amma wannan kuɗin sunan su Haram domin bata hanyar Halal a sa mesu ba‚ koda ko za gina masallaci ayi sadaka da kuɗin yana cikin haramci domin kuɗin sunzo ne ta Haramtacciyar hanya.
Al’umma da yawa sun fara shiga harkar zinace-zinace ne‚ da lilin tallata tsaraici da ake yi wannan zamanin. Ɗan ƙaramin yaro yasan waye mace? Haƙiƙa in kin kasance ɗaya daga cikin masu tallata tsaraici a Social Media koda ta hanyar rashin sanya Lulluɓin da ze rufe tsaracin ki ne‚ ki sani kuna zaluntar Salihan matan da ko ƙunsin su‚ basa bari wanda ba shi da hurumin gani ya gani. Domin kema mace ne sunan ki a zahiri‚ a baɗini ba lalai ki amsa sunan ki mace ba‚ domin kina yin aikin da bashi daga cikin siffar Mata. Kece mace kinfi kowa sanin kanki‚ don haka kin san mene ne ake kira tsaraici a tattare dake? Amma ba lallai kisan ke halitta ce mai daraja ba‚ har sai kin ki yaye wannan tsaracin naki, sannan za ki fara sanin ke Halitta ce mai daraja. Allah ya ƙara sanya kunya a cikin zuƙatan ƴaya mata ƙanne da yayyi da iyaye baki ɗaya.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku