Sojojin Najeriya sun ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok

KDK Hausa


Dakarun bataliya ta 114 na sojojin Najeriya sun ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da maharan suka sace a shekarar 2014.

 A ranar 14 ga Afrilu, 2014, 'yan ta'addar Boko Haram sun sace 'yan mata dalibai 276 a makarantar Sakandaren 'yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Borno.

 An kubutar da yawa daga cikin 'yan matan yayin da wasu ke tsare a hannun mayakan na boko Haram. 

 Yarinyar da aka ceto mai suna Hauwa Maltha, an ce an gano ta ne a ranar 21 ga watan Afrilu.

Domin karin bayani danna 👉 WANNAN 


0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku