Duk da nace mata ƴar uwa ni ba mai dalilin aure bace tace na yi mata posting idan ba baƙin ciki nake mata ba, ai followers ɗin Allah ne ya ba ni ba don nafi kowa ba, nace sauke yi haƙuri ƴan mata.
Bazawara ce da yaron ta ɗaya tana da ƴan ruwan shanta, kyakkyawa ce daidai gwargwado tana da kamun kan ta akwai gayu da izza da haƙuri.
Tana son aure miji wanda ba shi da mata ta rasu ko sun rabu matar ta yi aure ya zamo yana da yara daga biyu zuwa ukku, wanda uwar su ta yi aure ma, ya zamo yana da rufin asiri daidai kuma ba mummuna ba wanda bai da sha'awar tara mata.
Ya zama yana zama Abuja ko America ko England ko Saudia ko Madina ko Dubai ko ɗaya daga cikin ƙasashen waje masu kyau, bata da matsala tana da kuɗin ta da zata ja jari a ko'ina ne, za ta tafi da yaron ta ta haɗa da naka cikin amana, GOLDEN PEN YAR SAƘO CE.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN
Datti Assalafiy Yayi adalcin zance.
Akwai wani hira cikin bidiyo da ake yadawa a Facebook na wannan matar mai suna Layla Ali Uthman inda take cewa tayi aure har sau biyu, kuma itace ta nemi mazan da suka aureta akan su sake ta, bata son auren
Mutanen mu kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan matar mafi akasarin masu sharhi zaginta suke, BBC Hausa ne sukayi hira da ita, kuma ya kai shekara guda na saurari hiran a shafin BBC Hausa, a cikin dalilanta na kin auren ta nuna cewa akwai wani abu na ladabi ko kyautatawa da take ganin ba zata iya yiwa mijinta ba, tace misali da girki, don haka ta nemi rabuwa don kar ta sabawa hakkin aure
Ya kai shekara uku, lokacin muna tsakiyar yaki da 'yan Luwadi a Facebook, wannan matar ta samu wani yaro karami Almajiri an masa Luwadi, an lalata duburan yaron kuraje sun fito masa a duk jikinsa, da aka kaishi Asibiti aka tarar ya kamu da cutar hanta, wannan matar ita ta dauki nauyin jinyar yaron, ta mayar dashi yaronta, har yanzu yana hannunta da sauran wasu Almajirai da ta dauka tana kula da su
A lokacin nayi rubutu akan wannan mata bisa daukar dawainiyar Almajirin da tayi bayan 'yan Luwadi sun lalata shi na yaba mata na mata addu'ar alheri, ni dai tun daga wannan lokacin nake ganin kima da mutuncinta
Dalilin da yasa kenan yanzu da naga an bude sabon babi a kanta na ga ya dace nace wani abu, magana ta gaskiya, duk matar auren da ba zata iya yiwa mijinta biyayya ba to ta hakura da auren idan ta san zata iya kare kanta daga fadawa tarkon zina, sannan akwai matan aure da suke cin amanar aure, to da su tsaya gidan miji suna cin amanar aure yafi dan dama-dama su hakura da auren watakila zunubin yayi sauki, wannan a fahimtata kenan
Sannan akwai matan da zasu iya haduwa da lalura ta rashin lafiya a gidan aure, a wayi gari lalurar ya hanata mu'amalar aure da mijinta, sai mijin ya zama yana cutuwa, idan matar ta nemi saki babu laifi anan tunda shi kansa auren ba farilla bane a Musulunci
Kafin na gabatar da wannan rubutun sai da na gudanar da bincike na tambayi wasu da suka san Laylah a inda take a Abuja, sun fada min bayani na adalci akanta da irin tashi fadin da tayi har ta zama abinda ta zama yau a Abuja
Don haka shawara zuwa ga Laylah Ali Othman idan kina da wani boyayyen dalili da yasa kika nemi sakin aure wanda zai iya zama madogara mai karfi a gareki a gaban Allah to kina da uzuri, amma indai don a kan ba zaki iya yiwa mijinki girki bane yasa kika ki auren kamar yadda kika fada to wannan dalilin ba mai karfi bane, auren yafi miki komai daraja a rayuwarki, tunda kina da sauran kuruciya a tattare dake
Kuma indai batun girki ne, Musulunci bai tilasta mace dole ta dafawa mijinta abinci ba, mace ta dafawa mijinta abinci sannan ta masa wankin kaya yana babin kyautatawa ne kawai amma ba dole ba, kuma idan taki girka abinci babu zunubi, abinda Musulunci yace shine dole miji ya ciyar da matarsa abinci
Idan kuma wadanda suka aureki a baya sun zalunceki ne to ki sani akwai wasu maza a waje wadanda ba azzalumai ba, idan kina son dacewa da mazan kirki to ki gyara alakarki da Allah (T), sannan ki dage da addu'ah, wannan shawaran ya shafi dukkan 'yan mata da zawarawa
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN


0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku