Mutane suna dauka cewa namiji ya yage suturar mace da karfin tsiya ya sadu da ita shika dai ne ake nufi da fyade.
Toh tsaya kuji :
Kaga wannan yarinyar da tazo office dinka naiman aiki a company ka kace da ita sai ka kwanta da ita kafin ka bata aiki? Alhaji mai bada aiki mai fyade ne kai.
Kaga wannan yarinyar da ka kayar da ita jarabawa da gangan domin ka nemi ta baka kanta idan tana son taci jarabawa? Malam lecturer mai fyade ne kai.
Kaga wannan matar Abokin naka da tazo neman taimako wajanka saboda mijinta baida lafiya kace da ita, ki kaikaya mani bayana sannan in kaikaya maki naki? Malam mai kaikayi cikakken mai fyade ne kai.
Kaga wannan yarinyar da bata kai shekara 18yrs ba, kake saya mata drinks da indomie ka bata kudi ka kaita dakinka? Abokina kaima cikakken mai fyade ne kai.
Kaga wannan yar'uwar da tazo wajanka neman addu'a koh magani kace da ita ance ka kwanta da ita domin biyan bukatun ta? Fake pastor koh malamin tsibbu mai fyade ne kai.
Kaga wannan Budurwar da kuka hadu a motar haya kana matsaita saboda kana back seat zaune kusa da ita kana jin dadi har da lumshe ido kamar barayon kaza? Oga na back seat mai fyade ne kai.
Kaga wannan yarinyar da kake bin bayanta a layin ATM ko wajan screening koh registration daka mannemawa kamar wani cingam kana kawar da sha'awarka? Oga na layi mai fyade ne kai.
Mazaje da suka sami dama a hannunsu yawancin su duk masu fyade ne, domin sukan zubda ruwa a kasa ne dan su taka damshi.
Idan kace saboda shigar banza da mata keyi shike janyo yawaice - yawaicen fyade, toh ina kakai maganar Ubangiji daya ce ka runtse idonka idan kaga haramun? Kaga kenan kabi son zuciyarka ka sabawa wa Allah.
Da yawa daga cikinku masu fyade wata rana zaku haifa , koh ku tuba taubatan nasuha koh kuma ku saurari ranar da kuma zakuyi irin kukan da iyayen wadanda kuka lalata masu rayuwa suka yi.
allah kasa mudace mu gera zukatammu Ameen y ALLAH
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku