Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana cewa: "Akwai lokaci da zaizo wa al'ummah ta da zasu qaunaci abubuwa 5 su mance da abubuwa 5.
1. Zasu qaunaci Jin dadin duniya su mance da ranar lahira
2. Zasu qaunaci dukiya su mance ranar da za'a yi musu binciken abinda suka tara
3. Zasu ji tsoron abun halitta su mance da Mahallicin abun halitta
4. Zasu qaunaci manyan gidaje su mance da qaburburansu
5. Zasu qaunaci zunubi su manta da neman yafiyar Allah.
Shin lokacin baizo ba?
Wallahi yazo gashinan qarara muna gani.
Ya Allah Kayi dadin tsira, sallama, aminci da salati ga Cikamakin Annabawa, Shugaban Manzonni, Za6a66enKa, MasoyinKa, Wanda Ka aiko domin Zamewa Rahama ga dukkanin bayi, Mijin Khadija Angon Aisha, Uba ga Fatimah Baba ga Qasim, Aboki ga Abubakar Yaya ga Ali, Surukin Umar da Usamanu, Haske bisa Haske, Mafi soyuwa a zukatan masu imani sama da komai nasu, Mafi alherin masu alheri, Mafi tausayin masu tausayin, Mafi kyautan masu kyauta, Mafi saken fuskan masu sakin fuska, ba gajere bane balle ace mishi wada, ba dogo bane balle aga rama, shine Mafi kyauwan kyawawa, Ubangidan mu maganin kukan mu Annabi Muhammad dan Abdullahi (SAW) tsira da aminci su kara tabbata a gare shi.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN


0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku