Kungiyar PSG Ta Dakatar Da Messi Daga Wasa Na Tsawon Makonni Biyu
Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain ta dakatar da Lionel Messi na tsawon makwanni biyu ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakan ya faru ne biyo bayan tafiyarsa ba tare da izini ba zuwa Saudi Arabiya, bayan rashin nasara da suka yi da Lorient da ci 3-1 a karshen makon da ya gabata.
Romao ya wallafa hakan ne a shafinsa na Tuwita cewa: “Paris Saint-Germain ta yanke shawarar dakatar da Lionel Messi nan da nan na tsawon makonni biyu.
Dakatarwar za ta gudana ne a yanzu bayan tafiyar Messi zuwa Saudiyya ba tare da bada izini daga kulob din ba kamar yadda @RMCsport ta ruwaito. ”
Kocin PSG Christophe Galtier ya yi wa ‘yan wasansa alkawarin cewa za su samu hutun kwanaki biyu wato Litinin da Talata idan suka doke Lorient a ranar Lahadi.
Sai dai Galtier ya bayyana cewa rashin nasara zai sa ‘yan wasan za su je atisaye ranar Litinin.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku