A yau Litinin ne Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta fara zama domin sauraron ƙarar da ɗan takarar jam’iyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyar Labour, Peter Obi su ka shigar.
Ƴan takarar na kalubalantar zaɓen Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.
A zaɓen, Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, wanda ya samu kuri’u 6,984,520 da Peter Obi, wanda ya samu kuri’u 6,101,533.
A cikin ’yan takarar da ke kalubalantar nasarar Tinubu, Obi da Atiku ne suka fi fice.
Daily Trust ta gano cewa kotun ta yi cikar-kwari da lauyoyi da kuma magoya bayan ƴan takarar.
Chris Uche, SAN, shi ne shugaban kungiyar lauyoyin da za su kare Atiku yayin da Wole Olanipekun (SAN) ke jagorantar na Tinubu, sannan Levi Uzoukwu (SAN) shi ne shugaban tawagar Obi.
Domin karin bayani danna 👉 WANNAN

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku